Connect with us

News

Kamfanin da ke aikin titin Abuja zuwa Kano na son karin kudi N1.35tn -Ministan ayyuka

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Ministan ayyuka a Najeriya, Sanata David Umahi ya ce kamfanin gine-gine Julius Berger na neman sama da naira triliyan ɗaya domin kammala shimfiɗa babban titin Abuja zuwa Kaduna.

Da yake magana a wani taro da daraktocin ma’aikatar ayyukan a Abuja, babban birnin Najeriya, ministan ya ce titin da farko an ware naira biliyan 165 wanda aka ƙara kuɗin zuwa naira biliyan 654.

Advertisement

Yan-sanda a jihar Yobe sun An kama Malamin Jami’ar  bisa zargin kashe matarsa

Ya ce gwamnati ba ta da shirin biyan sabon farashin saboda rashin kuɗi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an ba da kwangilar aikin a shekarar 2017 amma sai a 2018 aka soma aikin.

Advertisement

Ya kamata a kammala titin cikin shekarar 2021 wanda ɗaya ne daga cikin ayyukan gwamnatin Buhari.

Sai dai hakan bai samu ba har gwamnatin ta sauka a 2023 amma dai an kammala fiye da rabin aikin titin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending