Connect with us

News

Kungiyar Kafafen Yada Labarai na Intanet Ta taya Gwamna Abba Murnar Samun Nasara A Hukuncin Kotun Koli

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Kungiyar kafafen yada labarai ta yanar gizo watoThe Association of Online Media Guild ta taya gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na jihar Kano murnar samun nassara a kotun koli.

A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa manema labarai ta hannun shugabanta na riko, Abdullateef Abubakar Jos da sakataren kungiyar, Abbas Yushau Yusuf.

 Saraki ya taya Gwamnonin Zamfara, Bauchi, Plateau da Akwa Ibom murnar samun nasara a kotun ƙoli 

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Juma’a ne Kotun Koli ta mayar da Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano bayan da kotun sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara suka soke nassara sa

Kungiyar ‘yan jaridu ta yanar gizo daga sassa daban-daban na kasar nan, hedikwatar ta a jihar Kano.

Advertisement

 

Kungiyar ta bukaci gwamnan jihar da ya kiyaye kyakkyawar alakar da yake da ita da ’yan jarida na yanar gizo, domin Kano ce ta biyu da ta samu dimbin kafafen yada labarai na yanar gizo baya ga jihar Legas.

Kungiyar Sun bukaci Gwamnan da ya kara inganta ayyukan more rayuwa domin cigaban jihar Kano.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending