Connect with us

News

Kisan Gilla: An Fara Binciken Sojoji Kan Kashe Fulani 11 A Kaduna

Published

on

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAHI

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta fara bincike kan kisan gilla da ake zargin dakarunta sun yi wa wasu Fulani 11 a yankin Ladduga da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna.

Advertisement

Shugabannin Fulani a kauyen Tilde Fulbe da ke Ladduga sun shaida wa wakilinmu cewa wani babban jami’in dan sandan sojoji mai muƙamin Birgediya-Janar ya je kauyen domin gudanar da bincike.

Zamu cigaba da baiwa gwamna goyon baya domin ayyukan cigaban Kano: Dan majalisa mai wakiltar Bebeji Hon. Ali Muhd Tiga.

A makon jiya ne wakilinmu ya ruwaito yadda aka tsinci wasu rubabbun gawarwakin Fulani 11 a dajin da ke kusa da yankin “Crossing” a karamar hukumar.

Advertisement

’Yan uwa da al’ummar garin tabbatar cewa gawarwakin na wasu Fulani 11 ne da sojoji suka kama a lokuta daban-daban a yankin.

Wani shugaban Fulanin Ladduga, Ayuba Muhammad ya shaida wa wakilinmu cewa ranar Asabar sojoji sun je gudanar da bincike a yankin.

Advertisement

Ya ce, “Ina tabbatar da cewa wani dan sandan sojoji mai muƙamin Birgediya-Janar ya zo, inda ya yi mana wasu tambayoyi game da kisan gillan.

“Mun kuma tabbatar masa da cewa mu ne muka ba wa kafar yada labarai ta Daily Trust duk bayanan da ke cikin rahoton da suka wallafa.”

Advertisement

Ayuba ya kuma tabbatar cewa babu wanda sojojin suka yi wa wata barazana a yayin binciken suka gudanar.

Tun bayan bullar rahoton dai masu fafutikar kare hakkin dan Adam suke ta kira da a gudanar da bincike kan kisan gillar da ake zargin sojoji sun yi wa Fulani 11 a yankin na Karamar Hukumar Kachia.

Advertisement

Aminiya ta ruwaito cewa wani lauya, Barista Muhammad Nura, ya ce sojoji ba su da hurumin kashe mutum ba tare da umarnin kotu ba.

Don haka ya bukaci Rundunar Tsaro ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin domin gano masu hannu a ciki da kuma hukunta su.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending