Connect with us

News

Hukumar EFCC ta sake bude babin binciken wasu tsofaffin gwamnoni 13

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kasa EFCC ta sake bude wani sabon babin bincike a kan wasu tsoffin gwamnoni da ministoci 13 da take zargi da aikata laifukan almundahana na sama da naira biliyan 853 da miliyan 800.

Advertisement

Jaridar punch da ta bankado labarin ta ce yanzu haka EFCC na gudanar da bincike a kan tsabar kudi na naira biliyan 81 da miliyan 600 da aka yi sama da fadi da su a ma’aikatar jin kai ta kasar.

Kisan Gilla: An Fara Binciken Sojoji Kan Kashe Fulani 11 A Kaduna

Kazalika akwai batun naira biliyan 2 da miliyan 200 da gwamnati ta ware dan siyan makamai da nufin yakar ayyukan ta’addanci da ke addabar kasar, toh amma maimakon haka, aka wawure kudin tare da yin amfani da shi ta hanyar da bata dace ba, kuma wadanda ake zargi sun hada da tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, wani shahararren dan wasa marigayi Raymond Dokpesi, sannan tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa akwai kuma tsohon ministan kudi na kasar Bashir Yuguda da dai sauran su.

Advertisement

Sanarwar EFCC ta kuma lissafa jerin tsoffin ministoticin da take gudanar da bincike a kan su, danage da abin da ya shafi almundahana da dukiyar kasa.

Akwai tsohon gwaman Zamfara Bello Matawalle, da a yanzu ke rike da mukamin ministan harkokin tsaro na kasar karkashin mulkin shugaba Bola Ahmad Tinubu da badakalar naira biliyan 70, sannan tsohon ministan albarkatun kasa kayode Fayemi da naira biliyan 4, akwai kuma tsohon gwamnan Ekiti Ayo Fayose da hukumar ke zargi da yin sama da fadi da naira biliyan 6 da miliyan 900.

Advertisement

Sauran tsoffin gwamnonin da binciken ya shafa sun hada da tsohon gwamnan Nasarawa Abdullahi Adamu da na Kano Rabiu Musa Kwankwaso, sannan tsohon gwamnan jihar Rivers Peter Odili da na Abia Theodore Orji, da na jihar Gombe Danjuma Goje sai Aliyu Wamako na jihar Sokoto, da na Bayelsa Timipre Sylva da kuma Sule Lamido na jihar Jigawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending