News
Yanzu-Yanzu: Emefiele Ya Garzaya Kotu, Ya Nemai A Sauya Sharuddan Belin sa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Yanzu haka dai tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya gurfana a gaban kotu domin neman a sauya masa sharudan belin sa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Ana dai tuhumar tsohon gwamnan na CBN akan wasu tuhume-tuhume shida da suka shafi badakalar tsabar kudi Naira biliyan 1.2.
NIN-SIM: Masu Hulda Da Kamfanonin Sadarwa Sun Koka Kan Katse Layinsu Daga Tsarin Kira
Wannan shi ne karon farko da Tsohon Gwamnan CBN zai bayyana a gaban kotu ba tare da wasu manyan jami’an tsaro dauke da makamai suna jagorantar shi zuwa kotun ba.
Idan za a iya tunawa an saki Emefiele daga gidan yarin Kuje a ranar 23 ga watan Disambar 2023, kwanaki 34 bayan alkali ya amince da bayar da belinsa.
Yana neman kotu ta sake duba wasu sharuddan belinsa.
Yanzu haka dai mai shari’a Hamza Muazu na babbar kotun birnin tarayya yana sauraron muhawara kan lamarin.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
