Connect with us

News

Shugabannin Jami’o’i sun ƙi yarda da wayon fincikar masu kuɗaɗe da ‘Yan Majalisar Tarayya ke ƙoƙarin yi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Majalisar Tarayya ta ce a soke ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa ɗaliban jami’o’i da na Kwalejojin Gwamnatin Tarayya

Advertisement

Shugabannin Jami’o’in Najeriya sun shirya tsaf domin bijire wa duk wani shiri ko asarƙala da Kwamitin Majalisar Tarayya ke ƙoƙarin yi domin fincikar masu kuɗaɗe, daga cikin tallafin shekarar 2024 na Naira biliyan 683 da Gwamnatin Tarayya ta bai wa jami’o’in.

Daga ‘yar buguwa kaɗan, sai likitocin Super Eagles suka ce wai guiwa ta ce ta gurɗe’

PREMIUM TIMES ta ji cewa shugabannin jami’o’in sun bayyana ƙin amincewar su da a taɓa masu kuɗaɗen, waɗanda a makon jiya Hukumar Tallafa wa Manyan Makarantu (TETFund), ta bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince a bai wa makarantun Naira biliyan 683 cikin 2024.

Advertisement

Ana dai sa ran cewa manyan makarantun za su warware matsaloli da dama ta hanyar yin amfani da kuɗaɗen, waɗanda sun nunka Naira biliyan 320 ɗin da gwamnatin Buhari ya ba su a cikin 2023.

Sai dai kuma masana da dama na ganin cewa ai adadin na Naira biliyan 683 ɗin ma cikin cokali ne, idan aka yi la’akari da irin matsalolin da jami’o’in ke fuskanta.

Advertisement

Yadda Jami’o’in Najeriya Za Su Kasafta Naira Biliyan 683:

Kowace jami’a za ta samu Naira biliyan 1.9.

Advertisement

Kowace Babbar Kwalejin Fasaha za ta samu Naira biliyan 1.1.

Manyan Kwalejin Ilmi Mai Zurfi kowace za ta samu Naira biliyan 1.3.

Advertisement

Katsalandan Daga Kwamitin Majalisar Tarayya:

Sa’o’i kaɗan bayan sanarwar da TETFund ta yi, sai Kwamitin Majalisar Tarayya ya rubuta wasiƙu ga kwamitocin Shugabannin Jami’o’i, na Shugabannin Manyan Kwalejojin Fasaha da na Manyan Kwalejojin Ilmi Mai Zurfi cewa kada su fara taɓa kuɗaɗen, har sai sun aika wa kwamitin abin da za su yi da kuɗaɗen an ba su amincewa daga kwamitin tukunna.

Advertisement

PREMIUM TIMES dai ta samu kwafen da Kwamitin Majalisar Tarayya ya aika wa Kwamitin Shugabannin Jami’o’in Najeriya.

“Muna buƙatar bayanan yadda za a kashe kuɗaɗen nan da ranar 23 ga Fabrairu, 2024.

Advertisement

“Za a aiko da kwafe 30 a rubuce. Sai kuma kwafe 30 a cikin faifan naɗar rubutu, wato soft copy.

“Za a aiko zuwa Sakateriyar Kwamitin Majalisar Tarayya, Ofis mai lamba 305, Hawa na 3. A Majalisar Tarayya.”

Advertisement

Ba a dai san dalilin da ya sa Kwamitin ya rubuta wannan wasiƙa ba, domin kowace makaranta dai ta na da ‘yancin kan ta ne bisa dokar Najeriya.

 

Advertisement

Amma dai wasu shugabannin na ganin cewa matakin da su Honarabul Onuoha suka ɗauka, wata dabara ce ta fincikar masu kuɗaɗe kawai.

Wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa wannan wasiƙa ta haifar da maganganu masu zafi a wani guruf na WhatsApp na Shugabannin Jami’o’i.

Advertisement

Sun riƙa yin raga-raga da ‘yan majalisa, su na cewa ba za su taɓa yarda su finciki kuɗaɗen jami’o’in su ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending