News
An Zabi Mace Ta Farko A Matsayin Shugabar Karamar Hukuma A Jihar Borno
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jam’iyyar APC ta lashe zabukan shugabannin kananan hukumomi da kansiloli 312 a daukacin kananan hukumomi 27 na jihar Borno.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yar takarar jam’iyyar APC a karamar hukumar Jere ta jihar, Inna Galadima, ta zama zababbiyar shugabar karamar hukumar, wacce ta zama mace ta farko da aka zaba shugabar karamar hukuma a jihar.
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 16, 4 sun jikkata A hanyar Kano zuwa Kaduna
Leadership ta ruwaito cewa Inna Galadima, wacce ta taba zama kwamishina kuma mai ba da shawara ta musamman, jami’in zabe na karamar hukumar Jere, Farfesa Mohammed Konto ne ya bayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaben.
Advertisements
