News
Har yau Najeriya na sahun gaba na lalatattun ƙasashen da rashawa da satar kuɗaɗen gwamnati ya zubar masu da martaba – TI
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Abun Mamaki, Kuna Iya Zama Ku Sulhunta Rigingimun ‘Yan Kudu, To Ita Arewa Me Tayi Maku Ne, Da Ba Zaku Zauna Ku Sulhunta Rigingimun Al’ummominta Ba? Daga Imam Murtadha Gusau
Sabuwar ƙididdigar da ƙungiyar Transparency International ta fitar, wadda ake auna martabar ƙasashen duniya da mizanin CPI, wato ‘Curruption Perception Index’ ya nuna cewa yanzu Najeriya ta can ƙasa, ita ce ta 145 a mizanin martabar ƙasashen duniya.
Babu wata yarjejeniya da muka kula da Tinubu — Gwamna Abba yusuf
Najeriya ta na ta 145 a cikin ƙasashe 180 da aka ɗora kan Sikelin Auna Rashawa da Cin Hanci, wato CPI.
Ana bai wa ƙasashe maki ne daga 100 abin da ya yi ƙasa har zuwa 0.
Hakan ya na nufin yawan makin ka, yawan mizanin martabar ƙasar a idon duniya, kuma ƙarancin satar kuɗaɗe da ƙarancin rashawa kenan a ƙasar.
Ƙarancin makin ƙasa kuwa na nufin nauyin ma’aunin ta na nufin lalacewar ta yi ƙamari sosai kenan.
Wannan mizanin dai na bin-diddigin shekarar 2023 ne, wanda kafin nan Najeriya ta na ta 150 ne.
Najeriya na sahun gaba wajen rashawa da satar kuɗaɗen al’umma, inda a awon mizanin CPI ta samu maki 24 a shekarar 2023, kamar yadda sabon lissafi ya nuna.
Najeriya ta ɗan cira sama, daga ta 150 a 2023 zuwa ta 145 a 2023.
Sai dai kuma TI ta birnin Berlin da ke Jamus ya ce babu wani bambancin a zo a gani daga makin Najeriya na 2022, wato 25, zuwa maki 25 na 2023.
Najeriya ta na koma-baya sosai a wasu ƙasashen Afrika, kamar Tsibirin Seychelles wanda ya samu mako har 71, sai Cape Verde mai maki 64 da Botswana mai maki 56.
Sai dai kuma ƙasashen Equatorial Guinea da Sudan da Somaliya sun fi Najeriya lalacewa, yayin da Equatorial Guinea ɗin ke da maki 17, Sudan 13 Somaliya kuma 11.
Najeriya na matsayi na 145 ita da Laberiya da Madagascar da kuma Mozambique.
Yawancin ɓangarorin da aka fi samun rahotannin koma-baya da tauye darajar Najeriya wajen cin hanci sun haɗa da ɓangaren shari’a, ‘yan sanda da manyan ɓarayin gwamnati.
