News
Nafi karfin naje gidan kurkuku dan gyaran Hali cewar abdulmajid dan bulki kwamanda
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fitaccen sojan Bakannan dake arewacin Nigeria Mai suna abdulmajid almustafa Wanda akafi sani da dan bulki kwamanda yace bazai taba chanza ra,ayin Saba Dan gwamnatin Jahar Kano ta kaishi kurkuku
Dan bulki kwamanda ya bayyanna hakanne lokacin da yake tattutunawa da wasu daga cikin masoyansa bayan da ya shagi iskar yancin fitowa daga gidan gyaran halin ayau alhamis
Kwamanda yace Wannnan halayen nawa maasu kyawune Kuma bazan taba chanzawa akan ra,ayin iyaye naba domin haka na gada a wajen mahaifina Dan nehu
Mahaifina ya kasance Dan santsi ne Kuma Mai taurin Kai ne akan dukkan abunda yasa a gaban cewar Dan bulkin
Adan haka Yace shi yanzuma ya daura damarar ga dukkan wata gwamnatin da zata kawowa Al,ummar ta cikas koda kuwa hakan zaiyi sanadiyyar komawarsa gidan gyaran hali Indai hakan zaisa jama,a zasuyi farin ciki da Kuma dorewar democradiyya
kamu kaini gidan yari da gwamnati tasa akayi na Kara daukar dorusa wajen sanin halin da Al,ummar suke ciki mussamman wadanna aka zalinta
Dan bulki kwamanda dai ana zarginsa da laifin tada zauna tsaye wajen fusata alu,ummar jahar Kano bayan wasu kalamai da jagoran darikar kwankwasiyya yayi ENG RABIU Musa kwanwaso yayi akan wasu daga cikin masarautun Kano kamar Yadda lauyan gwamnati ya ayyana
