News
Rundunar ‘yan sanda ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari a Hedkwatarta da ke Borno
DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA
Rundunar ‘yan sanda ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari a Hedkwatarta da ke Borno
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta musanta rahotannin da ke cewa an kai hari a Hedkwatarta da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno na arewa maso gabashin kasar.
Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da yawunta na jihar ta Borno ASP Nahum Daso Kenneth ya fitar ranar Asabar da maraice.
Rashin tsaro: ka magance ta’addanci ko ka yi murabus – Ƴan Najeriya ga Gwamnatin Tarayya
Kenneth ya ce ba a kai hari a “Hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jiha da ke Maiduguri ba” kuma tana karkashin kulawar jami’an tsaro sannan tana aiki.
Sai dai ya kara da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a Unguwar ‘Yan sanda da ke “garin Gajiram na karamar hukumar Nganzai” ranar 2 ga watan Fabrairu da tsakar dare lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu dakarunsu.
“Kwamishinan ‘yan sanda CP MI Yusufu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan sanda hudu da suka rasa rayukansu a yayin da suke kare Unguwar ‘Yan sanda ta Gajiram a Nganzai,” in ji sanarwar.
Borno na ci gaba da fuskantar hare-hare daga mayakan Boko Haram da na ISWAP wadanda suka kwashe shekaru da dama suna addabar jihar.
Mayakan sun kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu, baya ga sace mutane ciki har da dalibai.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
