News
Zafafan bayanan da Ribadu ya yi wa Sanatocin Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
PREMIUM TIMES ta samu cikakken bayanin da Mashawarcin Harkokin Tsaro na Musamman ga Shugaban Ƙasa, Nuhu Ribadu ya yi wa Sanatocin Najeriya, yayin ganawar sirrin su da sanatocin a ranar Talata.
Baya Ribadu, taron ya samu halartar sauran manyan jami’an tsaron Najeriya, sai kuma Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, na Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun, sai kuma Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Ibrahim Geidam.
DA ƊUMI-ƊUMI: Kungiyar kwadago ta sanar da yin zanga-zangar a fadin Nijeriya
Sun shafe sama da sa’o’i 9 su na ganawa, dangane da batutuwa na tsaro.
Majiya a wurin taron ta ce Ribadu ya jagoranci gabatar da bayanai, yayin da sauran manyan jami’an tsaron ƙasa ke yin ƙarin bayani a wuraren da suka dace su yi bayanin.
A jawabin da ya gabatar, Ribadu ya yi magana kan ƙungiyoyin ‘yan bindiga daban-daban a cikin ƙasar nan, da kuma irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen ganin ta shawo kan gagarimar matsalar.
BATUN ƘUNGIYOYIN TA’ADDANCI:
Ribadu ya ce hare-haren daƙile ‘yan ta’adda da daukarun Najeriya ke yi a Arewa maso Gabas sun rage farmakin ‘yan Boko Haram sosai.
Ya ce farmakin ‘yan Boko Haram ya ragu da kashi 8 a cikin watanni shida da suka gabata.
Ya ce a cikin 2023, Boko Haram sun kai farmaki sau 394, amma sau 64 an kai su ne lokacin mulkin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu. Sauran farmaki 330 kuma duk ƙarƙashin gwamnatin da ta shuɗe aka kai su.
Ya ce hakan na nuna irin ƙoƙarin da wannan gwamnati ke yi ne, wajen ta daƙile hare-hare.
Ya ƙara da cewa kuma hakan ya na nuna irin yadda ayyukan jami’an tsaro a yanzu ke tafiya bisa gagarimar samun nasara.
“Akasari a yanzu Boko Haram kai farmaki ne a wuraren da babu jami’an tsaro kusa, sai kuma dasa nakiya kan hanya, wanda hakan na nuni da cewa sun sauya dalo, sakamakon yadda dakarun sojoji suka takura masu da matsin lambar ganin sun kakkaɓe su.
Ribadu ya ce nazarin da gwamnati ta yi ya nuna Boko Haram ɓangaren ISWAP na fuskantar matsin lambar kasa kai hare-hare. Domin a cikin 2023, kashi 78 cikin 100 na hare-haren ISWAP, duk na kare kan su ne. Ya ce hakan na nufin a yanzu ba su iya kai hare-hare kamar da can a baya.
Ribadu ya gode wa Gwamnan Barno, Babagana Zulum, bisa dukkan taimakon da ya ke bayarwa wajen samun nasarorin da jami’an tsaro ke samu a yankin.
BATUN TSAGERUN IPOB:
Ribadu ya ce Najeriya ta samu gagarumar nasarar daƙile ta’addancin ‘yan IPOB a ƙarƙashin wannan gwamnati.
Ya ce ta hanyar yin amfani da ƙarfi da kuma shawarwari, hare-hare a Kudu maso Gabas ya ragu sosai da kashi 75 bisa 100 a cikin watanni shida.
Ya ce kafin a samu wannan nasara, a baya sun ƙone ofisoshin ‘yan sanda 164.
Ya ce amma a yanzu ba a zancen kai hari ofishin ‘yan sanda, sai batun gyare-gyaren waɗanda aka lalata ake yi yanzu.
Sannan ya ce dokar zaman gida tilas da IPOB ke ƙaƙaba wa mazauna yankin, kusan duk an daƙile su.
BATUN ‘YAN BINDIGA MASU GARKUWA:
Ribadu ya ce an samu ci gaba wajen ƙoƙarin daƙile ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Ya ce a watanni shida na ƙarshen 2023, hare-haren ‘yan bindiga ya ragu zuwa da kashi 45 bisa 100.
Ya ƙara da cewa yankunan karkasa da dama waɗanda a baya ba su iya zuwa gonakin su su yi noma, yanzu duk su na samun wannan damar.
Ya ce gwamnati ta yi nasarar karɓo sama da mutum 700 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a Arewa maso Yamma.
“A yanzu za ta iya tuƙa mota da dare zuwa daga Kaduna har Kano. An kakkaɓe mafi yawan gaggan ‘yan bindigar da suka addabi jama’a a yankunan,” inji Riba
Sai dai kuma har yanzu ‘yan bindiga na kai munanan hare-hare a Zamfara da Katsina.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
