News
DA ƊUMI-ƊUMI : An bindige Kakakin Yaɗa Labaran Jamiyyar APC na jiha a Pankshin
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An bindige Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC, Sylvanus Namang. An bindige Namang har lahira a cikin garin Pankshin, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Pankshin.
Shugaban APC na Jihar Filato, Rufus Bature, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da wannan kisan gilla da aka yi wa Namang.
Zamu sadukar da kanmu Domin cigaban Nigeria -sarkin gwandu na kebbi
Ya bayyana mamacin da cewa jajirtaccen gaske ne wajen ƙoƙarin kawo ci gaba ga APC a Jihar Filato da yankunan karkarar jihar baki ɗaya.
Bature ya ce APC na nan na shirin fitar da sanarwar kisan da aka yi wa Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar.
Wakilin mu ya gano cewa an bindige Namang a lokacin da ya ke tsaye ƙofar wani otal a garin Pankshin, wajen ƙarfe 7:30 na dare, a ranar Asabar.
Har yanzu ‘yan sanda ba su yi magana ba dangane da kisan da kuma dalilin kisan.
