Connect with us

News

Jami’an Tsaro Sun Mamaye Majalisar Dokokin JiharJigawa Kan Shirin Tsige Shugaban Majalisar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Jami’an tsaron hadin gwiwa sun karbe ikon majalisar dokokin jihar Jigawa a daidai lokacin da ake kokarin tsige kakakin majalisar Hon Aliyu Haruna Dangyating.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa ’yan majalisar na shirin tsige shugaban nasu ne saboda rashin gamsuwarsu da kuma zargin sa da yin babakere da yin gaban kansa wajen gudanar da harkokin majalisar da kuma rashin iya shugabanci.

Mbappe Zai Koma Real Madrid A Ƙarshen Kakar Bana

Bincike ya nuna goyon bayan da akasarin mambobin majalisar suka samu kan tsige shi ya haifar da fargaba a garin Dutse, babban birnin jihar.

Advertisement

Jami’an tsaron da aka tura harabar majalisar sun hana kowa shiga har da ma’aikatan majalisar.

Wani babban jami’in majalissar da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da an hana shi shiga harabar.

Advertisement

Matakin tsige shugaban Dangyating ya zo ne a daidai lokacin da yake kasar Saudiyya tare da gwamna Umar Namadi, a ziyarar da suka kai da nufin janyo masu zuba jari daga kasar zuwa jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa da aka tambaye shi game da tsauraran matakan tsaro, kakakin ’yan sandan jihar, DSP Lawal Shiisu Adam, ya ce sun samu bayanan sirri da ke nuna akwai barazana ga zaman lafiyar al’umma, lamarin da ya sa daukar matakan tsaro.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending