Connect with us

Sports

Lauyoyin matar da ta shigar da Alves kara sun ce sun gamsu da hukuncin da kotun ta Barcelona ta yanke.

Published

on

Dani Alves

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

 

 

Lauyoyin dan wasan Brazil Dani Alves sun ce za su daukaka kara kan hukuncin da wata kotu ta yanke masa bayan da ta same shi da laifin aikata fyade.

Bayan dage takunkumin da ecowas tayi Jamhuriyar Congo na,son Karfafa Zumuntar Hadin Gwiwa da china

Advertisement

A ranar Alhamis kotun ta samu Alves da laifin yi wa wata mata fyade a wani gidan rawa a Barcelona, ta kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru hudu da watanni shida a gidan yari.

Kotun Lardin Barcelona ta yanke wa tsohon dan wasan na Brazil da Barcelona dan shekaru 40 hukuncin ne bisa laifin yin fyade a ranar 31 ga Disamba, 2022.

Kotun ta yi la’akkari da cewa matar ba ta amincewa Alves ya sadu da ita ba, abin da ke nuni da cewa fyade ya yi mata.

Har ila yau, Kotun ta kuma umurci Alves da ya biya diyyar euro 150,000 ga matar, da kuma haramta masa zuwa gidan ta, ko kuma wurin aikin ta, ko kuma yin magana da ita ta kowace hanya har tsawon shekaru tara.

David Saenz wanda yana daya daga cikin lauyoyin da suka kare matar, ya ce, “sun gamsu da hukuncin.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending