Connect with us

News

Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Tinubu tsige wasu manyan jami’ansa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya gabatar mata ta neman tsige Mataimakin Babban Jami’in Hukumar FCCPC, Barrister Babatunde Irukera.

Wasiƙar da Tinubun ya aike wa Majalisar wadda Shugaban Majalisar ya karanto ta yayin zaman Majalisar a ranar Laraba, ta nuna Tinubu ya buƙaci tsige Irukera ne saboda rashin kataɓus.

Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi awon gaba da wasu masallata  cikin masallacin a Zamfara.

Dokar FCCPC ta tanadi cewa, sai da sahalewar Majalisar Dattawa kafin Shugaban Ƙasa zai iya tsige Mataimakin Babban Jami’in Hukumar.

Sanarwar da ta nuna tsige Irukera ta sake nuni da yadda Tinubu ya tsige Babban Daraktan hukumar Bureau of Public Enterprises (BPE), Alex Okoh, tare da sanar da waɗanda za su maye guraben waɗanda tsigewar ta shafa.

Advertisement

Bayan tafka zazzafar muhawara kan wasiƙar a zauren Majalisar, daga bisani Shugaban Majalisar, Sanata Apkabio ya ba da damar kaɗa ƙuri’ar jin ra’ayi wanda a ƙarshe waɗanda suka goyi bayan wasiƙar suka yi rinjaye.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending