Connect with us

News

VOA Hausa zatayi kawance da American university domin bunkasa yaran Hausa a fadin duniya duniya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

 

 

Jami’ar Maryam Abacha za ta horas da ma’aikatan Muryar Najeriya VON kyauta
Darakta Janar na Muryar Najeriya (VON), Jibrin Baba Ndace, ya bayyana shirin gidan rediyon na yin hadin gwiwa da Jami’ar Maryam Abacha wato American University of Nigeria (MAAUN) da nufin faɗaɗa manufar wannan jami’a ga kasashen duniya.

Ndace ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya kai wa shugaban jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ziyara a yammacin ranar Juma’a a Kano.

Advertisement

Ya ce tashar a shirye ta ke ta hada kai da mahukuntan jami’ar domin tallata sabuwar jami’ar ba a Najeriya kadai ba har ma da kasashen waje.

“A shirye nake in kasance a sahun gaba wajen tallata jami’ar, ba a Najeriya ba kadai ba har ma ga sauran kasashen duniya. Akwai labarai masu kyau da ke faruwa a Najeriya kuma daya daga cikinsu ita ce wannan jami’a.

“Muna da mutanen da suke yi wa kasarmu aiki tukuru don ci gabanta da kuma don ta bunƙasa ta fannoni da dama kuma Farfesa Gwarzo na kan gaba wajen haka. Daga yau labarin MAAUN zai kasance daya daga cikin abubuwan da VON ta sa gaba,” in ji Ndace.

Shugaban rukunin jami’o’in Maryam Abacha Farfesa Adamu Gwarzo, a jawabinsa ya bayyana cewa jami’sr za ta baiwa ma’aikatan VON ɗin horo na musamman kan yadda za du riƙa gudanar da ayyukan su, musamman a fannin yaɗa labarai da sauransu.

” Za mu tallafa muku matuƙa wajen ba ma’aikatanku horo. Kuma za mu yi haka ne kyauta ba tare da kun biya ba

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending