Connect with us

News

AZUMI :Rashin Wutar Lantaki A Jihar Kano Ya Rage Walwalar Jama’a A Watan Ramadan

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

A yayin da ake fuskantar matukar zafin yanayi da kuma ibadar azumin watan Ramadan, yanzu haka jama’a na ci gaba da kokawa bisa rashin tsayuwar hasken lantarki a fadin jahar kano.

Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa lamarin rashin rashin wutar lantarkin ya jefa al’uma da dama cikin mawuyacin hali.

Mai POS Ya Mayar Da N10m Da Wani Kwastomansa Ya Tura Masa Bisa Kuskure A Kano

Duk da cewa ’kanawa sun samu ingancin wutar lantarki a ‘yan kwanakin da suka gabata, sai ga lamarin ya dagule a ‘yan kwanakin da muke ciki, inda aka fara fuskantar matsalar a lokacin zafi, lamarin da ya haifar da rashin walwala a tsakanin al’umma.

Mazauna garin Beli dake karamar Hukumar Rogo a jihar kano sun yi matukar kokawa kan katsewar hasken latarkin musamman a  wannan watan na Ramadan

Wannan ya sanya mutane neman bayani dangane da halin kunci da suka samu kansu ciki daga kamfanonin da ke aikin rarraba wutar, sanadiyar rashin wutar.

Advertisement

Salim Bashir , wani mazaunin yankin Rogo local government ne a jihar kano ya baiyana cewa tun makon da ya gabata suka fara fuskantar matsalar wutar lantarkin.

Shi kuwa Abdullahi musa cewa ya yi makonni biyu rabonsu da samun wutar lantarki na tsawon sa’o’i uku a rana.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending