News
Shugaban Rasha Vladimir Putin Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Rasha Da Aka Gudanar Da Gagarumin Rinjaye
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba Vladimir Putin ya lashe zaben shugaban kasar Rasha da aka gudanar da gagarumin rinjaye, lamarin da zai ba shi wani karin wa’adi na mulki.
Sakamakon farko na kuri’un da aka kirga na nuni da cewa Shugaba Putin ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar da kaso fiye da 87 cikin 100 kamar yadda hukumar zaben kasar ta nuna.
Dole Ne A Hukunta Mutanen Dake Da Hannu A Kisan Sojoji A Jihar Delta -Majalisar Dattawa
Dw ta ruwaito cewa Fadar White House ta Amurka ta soki yadda sakamakon zaben tare da bayyana cewa an gudanar da zaben ne ba tare da ‘yan hamayya ba ganin cewar daukacin masu adawa da Shugaba Putin na tsare a gidan yari.
A ranar Lahadi aka kammala kada kuri’a a zaben shugaban kasar Rasha, wanda tun daga farko aka ayyana Shugaba Putin da ke cikin ‘yan takara a matsayin wanda ka iya lashe zaben.
Mai shekaru 71 a duniya, sakamakon zaben zai ba wa Shugaba Putin damar zarcewa kan madafan iko a wani sabon wa’adi na shekaru shida kan madfafan iko bayan ya kwashe shekaru 20 yana kan karagar mulki
-
News20 hours ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
