Business
Muna sane da tsare ɗanƙasarmu ma’aikacin Binance a Najeriya – Amurka
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Amurka ta ce tana da masaniya a kan rahotannin tsare ɗanƙasarta a Abuja, babban birnin Najeriya.
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta IHR Ta Bukaci Majalisa Ta Sasanta Da Abdul Ningi
A watan da ya gabata ne aka kama shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan tare da abokin aikinsa, Nadeem Anjarwalla, wanda ke da fasfon Birtaniya da Kenya a wani ɓangare na binciken kaucewa biyan haraji da gwamnatin Najeriya ke yi wa kamfanin na kuɗin kirifto.
Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, “A duk lokacin da aka samu wata matsala ta tsare ɗanƙasarsu a wata ƙasa, to ofishin jakadancin da ke ƙasar na yin duk mai yiwuwa wajen bayar da taimakon da ya dace.”
Ofishin jakadancin ya ƙi bayar da cikakken bayanai game da tsare ɗanƙasar, yana mai cewa saboda dalilai na sirri.
Yanzu haka Nadeem Anjarwalla, ba ya hannun Najeriya bayan da mahukuntan ƙasar suka tabbatar da cewa ya tsere, to amma wata majiya daga makusantansa ta ce ya bar Najeriya ne ta hanyar da ta dace.
Mahukuntan Najeriya dai sun ce suna aiki da jami’an tsaro don samar da takardar sammaci ga Mr Anjarwalla.
A ɓangare guda kuma, mahukuntan Najeriya sun maka kamfanin a gaban kotu inda suka shigar da tuhume-tuhume da suka shafi ƙin biyan haraji.
-
News1 day ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
-
News4 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
