News
Yanzu-yanzu:Wata Hatsaniya Ta Kaure Tsakanin Sojoji Da yan Adai-daita sahu
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata hatsaniya ta kaure tsakanin sojoji da matasa ‘yan Adai-daita sahu (Napep) a garin Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade a jihar Yobe, al’amarin da ya jawo raunuka a ranar Lahadi.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa a hatsaniyar ta faro ne sakamakon wata rashin jituwar da ta kunno kai tsakanin bangarorin biyu.
Wata majiya a Babbar Asibitin Kwararru da ke garin Gashuwa, ta bayyana cewa, an kashe mutum daya, yayin da mutum 9 suka samu raunuka daban-daban.
Majiyar ta kara da cewa, “Abin da ya faru shi ne motar sojojin ce ta zo a guje, inda ta yi kicibis da motar Golf, a kokarin kaucewa ne soja daya ya fado, inda motar sojojin ta kade wata Keke Napep, wanda hakan ya jawo sojojin daukar mummunan matakin.
“Wannan ya jawo matasan su ka harzuka tare da kulle babbar hanyar, ba shiga ba fita. Hakan ya jawo Shugaban Karamar hukumar Bade, Hon. Ibrahim Babagan Yurema, hadi da Maji-dadin Bade zuwa wajen domin baiwa matasan hakuri domin hana tashin-tashina.”
Duk kokarin jin ta bakin Rundunar ‘Yansandan jihar Yobe kan batun ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, lamarin ya cutura.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
