Connect with us

News

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano Ta Sake Gurfanar Da Ganduje A Gaban Kotu

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauraron korafe-korafen jama’a ta jihar Kano ta shigar da sabbin tuhume-tuhume kan almundahana a kan tsohon gwamnan jihar Dr. Abdullahi Ganduje.

Leadership ta ruwaito cewa Shugaban Hukumar, Muhuyi Magaji ne ya bayyana hakan a shirin ‘Sunrise Daily’ na gidan talabijin na Channels a ranar Talata, inda ya zargi gwamnatin Ganduje da karkatar da kudaden al’umma.

‘Yan Sanda Sun Kama Matar Da Ta Yi Karyar Garkuwa Da Ita Sannan Ta Yi Wa Kanta Farashin Kudin Fansa

Ya bayyana cewa, bincike ya nuna yadda aka karkatar da naira biliyan 51.3 na kudaden kananan hukumomi zuwa wasu asusun ajiya da basu da hurumin karbar irin wadannan kudaden.

A cewar Muhuyi, gwamnatin Ganduje na cire naira biliyan 1 a duk wata daga asusun jihar ba bisa ka’ida ba.

Ya kuma yi ikirarin cewa, an zuba Naira biliyan 4 ga asusun wani kamfanin noma daga asusun tattara harajin jihar ba tare da wani dalili ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending