Politics
Jam’iyyar Nnpp Ta Dakatar Da Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Jihar Kano Daga Cikin Jam’iyyar.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Tsagin jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Major Agbo ya sanar da dakatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano daga cikin jam’iyyar.
A cikin sanarwar da Ogini Olaposi, sakataren jam’iyyar, ya fitar a yayin taron ‘yan jarida na wannan Talata a Abuja, tsagin jam’iyyar ta NNPP, ya ce rashin bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi shi ne ya sanya su daukar wannan mataki.
Ƴan Najeriya miliyan 95 ne ke buƙatar yin rajistar katin shaidar ƙasa – HukumarNIMC
Jaridar The Punch ta ce tsagin na NNPP ya fusata da halartar babban taron jam’iyyar da wani bangare karkashin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya jagoranta da gwamnan na Kano ya yi a ranar 06.04.2024.
A jawabin Mr. Olaposi, ya ce ba su ga dalilin da gwamnan Kano zai halarci taron na Kwankwasiyya da a ganinsu haramtacce ne ba. Sai dai tuni wasu ‘yan Kwankwasiyya suka yi watsi da wannan dakatarwa daga jam’iyyar ta NNPP wacce a karkashinta ne aka zabi gwamnan na Kano da kuri’u sama da miliyan daya.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
