Connect with us

News

Da Dumi Dumi: Gwamnatin Jihar Kano ta Rufe Wani Asibiti Mai Zaman Kansa   

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar dake kula da asibitoci masu zaman kansu ta jihar Kano (PHIMA) ta rufe wani asibiti mai suna Sassauka Clinic and Diagnosis Centre, dake unguwar Rimin Kebe  a jihar Kano.

Advertisement

Da yake bayyana dalilan da suka sanya aka rufe asibitin, babban daraktan hukumar ta PHIMA, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon saba wasu dokokin hukumar da asibitin ke yi.

Rashin Ruwa: Yadda Matsalar Ruwan Sha Ta Addabi Kanawa

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano Ibrahim Abdullahi ya turawa da Jaridar Inda Ranka

Advertisement

Farfesa Salisu ya bayyana cewa an sauyawa asibitin suna ba tare da sanar da hukumar ba, Inda yace da farko hukumar ta yiwa asibitin rajista ne da sunan Sassauka Clinic and Diagnosis, amma yanzu kuma asibitin ya koma yana amfani da wani sunan na daban inda ya koma Sassauka Hospital ba tare da neman sahallewar hukumar ba, wanda hakan ya sawa doka.

Shugaban hukumar ya kara da cewa an kuma kara fadada asibitin daga mai gado shida ya koma mai Gado 40 ba tare da sun sanar da hukumar ba, wanda shi ma hakan ya sabawa dokar hukumar.

Advertisement

Ya kuma bayyana cewa, a dokar hukumar duk asibitin da yake da gado 40 dole ne ya samar da akalla likitoci guda 3, Amma yace su asibitin Sassauka har yanzu likita daya ne ke kula da shi kuma shi ma ba kullum yake zuwa ba.

Farfesa Salisu ya koka da cewa hatta ma’aikatan da ke tallafawa wajen tafiyar da asibitin sun yi ƙaranci kuma hakan yasa bawa ka’idar aiki.

Advertisement

Shugaban ya ce saboda wadancan laifukan da aka lissafa ne yasa suka rufe asibitin kuma suka gayyaci mai asibitin zuwa hukumar a mako mai zuwa domin daukar matakan da suka dace akan shi.

Daga nan sai shugaban hukumar ya nanata kudirin hukumar PHIMA na ci gaba da tsaftace ayyukan asibitoci masu zaman kansu a jihar, inda ya bukace su da su ba hukumarsu hadin kai domin cimma burin da aka sanya a gaba, wanda ke samar da ingantacciyar hidimar kiwon lafiya ga jama’a.

Advertisement

Ya yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kyakkyawar kulawar da ya baiwa tsarin kiwon lafiya na jihar ta hanyar samar da kayan aiki da ake bukata domin farfado da fannin domin ya dace da tsarin aikin kula da lafiya a duniya.

Farfesa Salisu ya kuma yaba da irin goyon baya da jagoranci da Kwamishinan Lafiya Dokta Abubakar Labaran ya bai wa hukumar ta PHIMA da sauran hukumomin da ke karkashin ma’aikatar wajen gudanar da ayyukansu ba tare da tsoma musu baki ba .

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending