Connect with us

News

Hukumar EFCC Ta Kama Tsohon Ministan Jiragen Sama Hadi Sirika

Published

on

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rahotanni sun nuna cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki ta kama tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.

Advertisement

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Hukumar ta EFCC ta kama Sanata Hadi Sirika ne kan zargin badakalar Naira biliyan 8.06 a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Dangin Amarya Sun Hallaka Dan Bindiga Yayin Da Suka Dakile Yunkurin Garkuwa Da Mutane A Jihar Zamfara

Wasu jami’an hukumar sun ce an kama shi ne a ci gaba da binciken da EFCC ke yi kan ma’aikatar sufurin jiragen sama a lokacin shugabancinsa.

Advertisement

Hadi yana fuskantar zargin almundhanar kwangila, karkatar da kudade, amfani da ofishinsu ta hanyar da ba ta dace ba da kuma safarar kudaden haram.

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Talata EFCC ta tsare shi, bayan ya gabatar da kanta a babban ofishinta da ke Abuja domin amsa tambayoyi.

Advertisement

Ya je amsa tambayoyi ne kan zargin ba Engirios Nigeria Limited mallakin kaninsa mai suna Abubakar kwangilar makudan kudade.

Ya ba wa kanun nasa kwangila ne duk kuwa da cewa kanin nasa ma’aikacin gwamnati.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending