News
Yadda Ɗan Shekara 12 Ya Bindige Ƙanin Sa Dan Shekara 6 Bisa Kuskure A Taraba – ‘Yan Sanda
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta bayyana cewa wani yaro dan shekara 6, dan uwansa mai shekaru 12, ya harbe shi bisa kuskure a Jalingo babban birnin jihar Taraba. (PREMIUM TIMES ta boye sunayen yaran saboda kananan yara ne).
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a garin Nukkai, a babban birnin jihar.
Al’ummar Allawa Da Ke Jihar Neja Na Tserewa Daga Gidajensu Bayan Janye Sojoji Daga Garin
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis a Jalingo, kwamishinan ‘yan sandan jihar, David Iloyanomon, ya ce an kama iyayen yaran tare da mika lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) na ‘yan sanda a jihar domin gudanar da bincike.
Ya ce akwai kuma irin wannan lamari na kisan kai da ya shafi yara kanana wanda kuma aka gayyaci iyaye da masu kula da su domin yi musu tambayoyi.
Ba za a iya tuhumar ƙananan yara kan laifin kisan kai ba. Shi ya sa aka tasa keyar iyaye da masu kula da yaran da suka bar bindigogin a inda yarannza su iya kaiwa ga su, an mika su zuwa CID na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi.
Mazauna garin Nukkai sun ce lokacin da suka ji karar harbin, sun yi zaton masu garkuwa da mutane ne suka diran musu.
Wannan lamari dai ya faru ne makonni kadan bayan kashe yara uku a kauyen Didango Geit da ke karamar hukumar Karim-Lamido ta jihar sakamakon irin wannan ganganci da suka yi a tsakanin su a gidajen iyayen su.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
