Connect with us

News

Ƙaƙaniƙayin Bashi Ya Sa Matashi Basajar Sake Shiga Musulunci

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Jihar Kano ta bayar da umarnin yi wa Haruna Abdulkarim mai shekaru 25 bulala goma don ladabtar da shi bisa laifin ƙaryar shiga musulunci.

Advertisement

Jami’an Hisbah yankin ƙaramar hukumar Kura su ne suka damko Abdulkarim.

CBN ta janye daga karawa Yan Najeriya harajin kuɗi bisa umarnin Shugaba Tinubu. 

Wikki Times ta ruwaito cewa cewa Duk Juma’a ana ganin shi yana zuwa Masallaci a ƙoƙarin sa na ƙaryar ƙwadayin son shiga Musulunci, tare da neman taimakon sadaka sakamakon hakan da yake yi ya sa kwamandan Hisbah na karamar hukumar Kura Ali Alkasim ya ba da umarnin a kamo shi tare da mika shi ga yan sanda.

Advertisement

 

Nan take aka gurfanar da shi a gaban kotu tare da tuhumar sa laifin da ake zargin ya aikata.

Advertisement

Bai musa ba ya amsa laifin sa tare da bayyana cewa tsananin bashi ne ya sa shi jefa kanshi cikin wannan hali. Sai dai ya roki a yi masa sassauci, inda ya sha alwashin ba zai sake irin wannan halin ba

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending