News
Nasir El Rufa’i Yakamata Ku Gayyato Domin Yazo Ya Yi Jawabin Inda Ya Saka Dukiyar Kaduna Amma Ba Tsoffin Kwamishinonin Sa Ba —Shehu Sani
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook Yana Mai cewa kwato ku’din rancen da bankin duniya ya bayar na dala miliyan 350 da Yan Kaduna suka wawure ba za a iya samuwa ba ta hanyar gayyata da yi wa tsofaffin kwamishinoni da masu ba da shawara tambayoyi, ba tare da gayyato tsohon Gwamna El rufa’i da kuma yi masa tambayoyi ba.
Don amsa tambayoyi kan bashin; tare da bayyana inda aka dawo da Kason Kaduna na Paris, Excess Crude Funds, Stamp Duties Funds, Ecological Funds da Billions a lamunin da aka karba daga Babban Bankin da Bankunan Cikin Gida.
Duk ’yan kwangila da masu ba da shawara marasa amfani da suka kwashe kudi suka gudu da duk wanda ya ci moriyar rabon kadarorin Jihar Kaduna kuma har yanzu suna cin moriyar hakan da kansu.
ko da ike Allah yaso ba Comrade Shehu Sani don ba ne Ba ni da lokacin yin wasanni Inji Tsohon Sanatan.
Akwai adawar Siyasa Mai karfi tsakanin Sanata Shehu Sani da Tsohon Gwamna Nasir El rufa’i.
