Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya ta gano ‘haramtattun’ matatun man fetur 50 da ake aikin tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Hukumomi a Nijeriya a ranar Lahadi sun ce sun gano wasu haramtattun wurare 50 da ake aikin tace man fetur ba bisa ƙa’ida ba.

Advertisement

Rear Adm. John Okeke, kakakin rundunar ‘Operation Safe Delta’ da take aiki a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur na kasar, ya ce sojoji na ci gaba da kai hare-hare kan masu fasa kwabrin mai a yankin.

Karin kudin wutar lantarki: Kungiyar Kwadago ta NLC Ta Lashi Takobin Zaman Dirshen A Gaban Ofishin Hukumar NERC A Gobe

Okeke ya lura cewa an kama man fetur mai yawa sosai da aka sace.

Advertisement

Ƙaruwar satar man fetur da ake yi a Nijeriya na yin illa ga tattalin arzikin kasar.

Wani ɗan majalisar dattijan ƙasar, Sanata Ned Nwoko a baya ya taɓ bayyana cewa kasar ta yi asarar sama da dala biliyan uku a shekarar 2023 sakamakon ƙaruwar satar mai da hare-hare kan bututan mai.

Advertisement

Arzikin man fetur da Nijeriya ke da shi ya kai kusan ganga biliyan 37, wanda ya zama kashi 3.1% na yawan wanda ake adane da shi a duniya.

A matsayinta na daya daga cikin kasashe 15 masu arzikin ɗanyen mai a duniya, Nijeriya tana matsayi na takwas a fannin arzikin man da aka tabbatar, sannan ta shida wajen fitar da mai.

Advertisement

Yankin na Delta, inda ake da rijiyoyin mai, yana fama da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke yin zagon ƙasa a rijiyoyin mai, lamarin da ke haifar da rigingimu da garkuwa da mutane da sauran tashe-tashen hankula a yankin.

 

Advertisement

Trt Afrika

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending