News
Karin kudin wutar lantarki: Kungiyar Kwadago ta NLC Ta Lashi Takobin Zaman Dirshen A Gaban Ofishin Hukumar NERC A Gobe
DAGA MUHAMMAD YASIR KABIRU
Kungiyar kwadagon Nijeriya ta lashi takobin zaman dirshen a gaban ofishin hukumar NERC mai kula da farashin lantarki tare da rufe kamfanonin rarraba lantarki har sai sun janye sabon karin kudin lantarkin da suka yi a baya-bayan nan.
Daily Post ta ruwaito cewa Karin kudin wutar lantarki: NLC za ta dauko DISCOs, ofisoshin NERC a ranar Litinin
Shugaban Rasha Vladimir Putin Ya Sauke Ministan Tsaron Ƙasar Sergei Shoigu Daga Muƙaminsa
Kungiyar kwadagon Nijeriya ta lashi takobin zaman dirshen a gaban ofishin hukumar NERC mai kula da farashin lantarki tare da rufe kamfanonin rarraba lantarki har sai sun janye sabon karin kudin lantarkin da suka yi a baya-bayan nan.
Kungiyar ta NLC ta ce mambobinta rufe kamfanonin rarraba wutar lantarki DISCOs, a duk fadin Najeriya.
Umarnin ya biyo bayan taron kwamitin CWC, a ranar 30 ga Afrilu, 2024.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren kungiyar NLC, Chris Uyot, ta ce: “An shirya rufewar ne a duk faɗin ƙasar a ranar Litinin, 13 ga Mayu, 2024.”
Kungiyar kwadagon ta rubuta wasikar zanga-zanga zuwa hedkwatar NERC inda ta ba da wa’adin ranar 12 ga Mayu, 2024 cewa NERC ta sauya karin kudin wutar lantarki ko kuma a dauki matakin gaggawa.
Kungiyoyin sun bayar da misali da halin da ake ciki na cewa matakin NERC zai ingiza al’umma sabida Tsadar rayuwa
Sun bayyana cewa karin kudin da aka sanar ba wai ya sabawa tsarin da doka ba, har ma da take hakkin ‘yan Najeriya.
