News
Abinda Atiku, Obi, Saraki da Lamido suka tattauna a ganawar sirri da suka yi a Abuja
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, da takwaransa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, sun yi ganawar sirri a Abuja ranar Litinin.
Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ne, ya wallafa hotunansa tare da Obi a yayin ganawar a kan X.
Mutane uku sun rasa ransu sakamakon rikicin kauraye a wurin gangi a Kano
Premium Times ta ruwaito cewa Obi ya kuma yi wata ganawa ta daban da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.
Obi ya kuma yi wata ganawa ta daban da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.
A cikin wata sanarwa bayan tarurrukan, mai magana da yawun yakin neman zaben shugaban kasa na LP, Tanko Yunusa, ya ce Mista Obi ya ziyarci Messrs Abubakar (Atiku), Saraki da Lamido don tattaunawa kan “yanayin kasa”.
“Dangane da halin da al’ummar kasar ke ciki da kuma karuwar rashin tabbas na rayuwar talakawa da marasa galihu, Obi a ranar Litinin ya ziyarci wasu jiga-jigan ‘yan Najeriya, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.
Bayan haka Obi ya tattauna matsalolin rashin zaman lafiya, ta’addanci da garkuwa da mutane da suka addabi ƴan Najeriya musamman yankin Arewa.
Wannan shine ziyarar farko da Obi na LP ya kaiwa jigajigan PDP tun bayan zaɓen 2023.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
