News
Nijeriya Ce Koma Baya A Kasafin Kuɗin Ilimi A Yammacin Afirka –Kungiyar ASUU
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ta ASUU, ta yi Allah-wadai da yadda ake nuna halin ko-in-kula da harkar ilimi, inda ta ce Nijeriya ce a ƙarshe a kasafin kuɗin ilimi a yankin yammacin Afirka.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka a taron yini ɗaya kan ‘Bukatun Ɗalibai masu tasowa a Cibiyoyi’, wanda Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund) ya shirya a Abuja ranar Talata.
Gwamnatin Shugaba Tinubu Ce Silar Rugujewar Najeriya -Babachir Lawal
Ya kuma nanata kiran da ƙungiyar ta yi na sake duba harajin ilimi zuwa kashi 10 cikin 100, yana mai cewa za ta kara kuɗaɗen TETFund daga Naira biliyan 600 a duk shekara zuwa Naira tiriliyan uku.
“Mun gudanar da bincike kan ƙasashen yammacin Afirka. Mafi ƙarancin kasafi ga ilimi da kowace ƙasa a Afirka ta Yamma ke bayarwa shi ne kashi 15 cikin 100. Mafi girma shi ne kashi 32 cikin ɗari.
“Muna cikin ƙasar da muke bayar da kashi 4.5 zuwa 7 cikin 100 wanda kasa da kashi 70 cikin 100 ake sakin su. Amma gwamnatin Awolowo tana ware sama da kashi 30 na ilimi,” inji shi.
Ya kuma bayyana jihohin Enugu da Abia da kuma Oyo da ke ware sama da kashi 20 na kasafin su a fannin.
Mista Osodeke ya caccaki shugabannin jami’o’in da dama saboda gazawarsu wajen ɗaukar masu ruwa da tsaki wajen yin amfani da kuɗaɗen da ake baiwa makarantunsu na TetFund.
“Hukumar TETFund da ta gayyace mu a matsayin masu ruwa da tsaki zuwa wannan taro misali ne na yadda ya kamata a tafiyar da al’amura.
“Mun yi taron kwamitinmu na ƙasa (NEC) kwanakin baya, kasa da kashi 10 cikin 100 ne suka kira taron masu ruwa da tsaki.
“Ina so in yi kira ga duk jami’ar da ba ta ɗauki masu ruwa da tsaki ba, to kada a bar ta ta samu damar shiga asusun. Kuɗaɗen na al’ummar Nijeriya ne,” inji shi.
