Connect with us

News

Cakwakiya: Wani Mutum Da Ke Ibada A  Wata Coci Ya Debowa Pasto Din Cocin ‘Yan-sanda

Published

on

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Wani mutum da ke ibada a wara coci ya debowa Pasto din cocin ‘yan-sanda, bayan da Paston ya ki mayar masa da kudinsa da ya tura masa bisa kuskure.

Jaridar Nigeria Jounal ta ruwaito cewa Tun farko dai mutumin ya yi alkwarin bai wa cocin kudin tallafin nan da kiristoci su ka saba bayarwa da ake kira Tithe da turanci.

Sai dai garin tura naira dubu dari daya sai yayi kuskuren tura naira miliyan daya, wannan lamari shi ya sa ya bukaci paston da ya dawo masa da dubu dari 9.

Tunda dai dubu dari daya yayi niyyar biya, sai dai Pasto ya ce sam shi fa bai san wannan zance ba, domin mutumin ba kuskure ya yi ba, abin da ya kamata ya bai wa cocin ne ya yi kwaro shine Allah ya kama shi. Saboda haka kudin nan sun ciwu.

Wannan lamari ya fusata mutumin ya garzaya ofishin ‘yan-sanda aka zo aka kama Pasto

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending