News
Zafin Rana Mai Tsanani Tana Cigaba Da Hana Kanawa Walwala
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Zafin rana mai tsanani da ake fama da shi a jihar Kano na cigaba da hana jama’a walwala saboda rashin samun kariyar da ya kamata su yi wa kansu.
A wannan lokaci da zafin ranar kan zarta degree 40 a ma’aunin zafi, babu abunda jama’a suka fi yi face yawaita shan ruwan sanyi da wanka da ruwan sanyin, a daidai lokacin da suke cigaba da gudanar da harkokinsu a takure.
Direbobi da ke tafiya mai dogon a yankin arewacin Najeriyar, sun koka da yanayin na zafi, sai dai sun ce idan suka tsaya ne lamarin yafi yawa, domin a yayin da suke tafiya iska na dan fifitasu.
Wasu ‘yan kasuwa da ke tafiyar da harkokinsu na kasuwanci a kan ranar kuwa, sun koka da hali mawuyaci da suke ciki, inda wasu kan koma gida su dan watsa ruwan sanyi, kafin su sake komawa bakin harkokinsu na kasuwanci. A yayin da wasu da ba zasu iya komawa gida ba kan bi inuwa inuwa domin samun saukin lamarin.
Su ma dabbobi a ba a barsu a baya ba na jin radadin yanayin na zafi, saboda karancin abinci.
Akwai dai rahotannin da suka nuna yadda al’umma a wasu jihohin Arewacin Najeriya kamar Kano da Maiduguri da Sokoto da Adamawa dadai sauransu, su ka yi matukar kwaluwa da hasken Rana mai dan karen zafi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
