Connect with us

News

Shugaba Tinubu Zai Gabatar Da Jawabi A Zaman Hadin Gwiwa Na Majalisar Dokokin Kasar A Gobe Labara 

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yana gabatar da jawabi a zaman hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

A ranar Laraba ne shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai gabatar da jawabi a zaman hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar domin murnar cika shekaru 25 na mulkin dimokradiyya da ‘yan majalisar dokoki a Najeriya ke yi.

Sani Tambawal magatakardan majalisar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin.

Advertisement

‘Yan-sanda sun kama mutane 13 ciki har da sojoji 4 da wani jami’in Civil Defense da laifin fashi da makami.

Ya kuma ce shugaban kasar zai kaddamar da sabon dakin karatu da aka gina a majalisar dokokin kasar.

Wannan don sanar da Sanatoci da Mambobi ne cewa a wani bangare na taron tunawa da shekaru 25 na mulkin dimokradiyya da ‘yan Majalisu a Najeriya, za a yi zaman hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da na Wakilai a ranar Laraba 29 ga watan Mayu, 2024.

Advertisement

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi a taron hadin guiwa kan harkokin kasa da kuma kaddamar da dakin karatu na majalisar dokoki ta kasa.

“Sanatoci masu girma da masu daraja ana sa ran za su zauna da karfe 9 na safe.”

Advertisement

Kafin yanzu dai an mayar da jawabin zaman hadin gwiwa na majalisar zuwa gabatar da kasafin kudi na shekara.

Amma shekaru 25 na dimokuradiyyar da ta katse da alama ta gabatar da wani muhimmin mataki na bikin.

Advertisement

Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya a shekarar 1999 tare da rantsar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar 29 ga watan Mayun 1999.

Wannan jamhuriya a yanzu ita ce mafi dadewa tun bayan samun ‘yancin kai a 1960, domin ta wanzu ba tare da kutsawa cikin sojoji ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending