News
Wata Kotu ta ba da umarnin kwace dala miliyan 1.4 da ke da alaka da Emefiele
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta sake bayar da umarnin kwace wasu makudan kudade da Kimar,su takai Dala Miliyan 1.4 na wucin gadi da aka alakanta da tsohon.. gwamnan .babban bankin Nigeria Godwin emefele
Mai shari’a Ayokunle Faji ya bayar da wannan umarnin na kwace kudaden ga gwamnatin tarayyar Najeriya.
Alkalin ya kuma umarci hukumar EFCC da ta buga wannan kudiri na wucin gadi a wata jarida ta kasa domin duk mai sha’awar kudin da ake nema ya bayyana a gaban Kotu tare da nuna dalilinsa cikin kwanaki 14 da ya sa ba zai zama na karshe na kwace wadannan kudaden.
Advertisements
