Connect with us

News

Yadda Dagaci ya karbi N700,000 ya bari ‘yan bindiga suka kashe jama’a masu yawa a kauyensa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa ta’addanci ya zama wani kasuwanci da wasu manyan mutane daban-daban ke cin ribar sa.

Advertisement

A wani faifan bidiyo da ya karade dandalin sada zumunta, gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa bai fahimci haka sha’anin ‘yan bindiga keda sarkakiya ba sai bayan ya zama gwamnan Jihar Katsina.

Kamfanin wutar lantarki zai katsewa hedikwatar ‘yan Sanda da barikin sojoji wuta saboda bashi

Dikko Radda ya bayyana cewa “hatta mutanen da baka taba tunani ba akwai hannunsu a wannan matsala ta ‘yan bindiga da muke fama da ita a jihar nan”.

Advertisement

A wata hira da ya yi da Jaridar Vanguard bayan cikar sa shekara guda a kan mulki, Dikko Radda ya yi waiwaye a kan irin abubuwan da suka gani a kokarin gwamnatinsa na yakar ta’addanci da ‘yan bindiga.

Da yake karin bayani a kan hakan, Dikko Radda ya bayyana yadda wani Dagaci, a wani kauye da bai bayyana sunansa ba, ya karbi cin hanci daga wurin ‘yan bindiga domin ya bari su shiga garinsa su ci karensu babu babbaka, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutanen kauyensa 30.

Advertisement

Wikki Times ta ruwaito cewa Gwamnan ya kara da cewa talauci yana taka rawa sosai wajen kara rura wutar rashin tsaro a jihar. A cewarsa, abin takaici ne yadda talauci ke saka wasu mutane bawa ‘yan bindiga muhimman bayanai a kan N2,000 kacal.

A karshe, Dikko Radda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yakar talauci a jihar Katsina domin ganin batagari basu cigaba da amfani da talauci domin cimma miyagun manufofinsu ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending