Connect with us

News

Wata Dalibar Jami’a Ta Jefo Jariri Da Ta Haifa Daga Bene Jim Kadan Bayan Haifarsa A Cikin Bandaki.

Published

on

DAGA NUASIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Wata daliban Jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse a jihar Jigawa da jefo jaririn da ta haifa daga bene Jim kadan bayan haifarsa a cikin bandaki.

Advertisement

Wani dalibi a Makarantar ya shaidawa Jaridar GLOBAL TRACKER cewa dalibar da aka sakaye sunanta ana zarginta da kulle kanta a bandakin dakunan Mata na makarantar inda ta haihu, kafin daga bisani ta jefo jaririn da cikin bandakin dake dakunnan dalibai na sama.

Rahotanni sun bayyana cewa dalibar dake tsangayar koyar da harkokin Noma na Jami’ar tana aji na biyu ne.

Advertisement

Rundunar Yan Sandan jihar ta bakin kakakinta DSP Lawan Shiisu Adam ya ce tuni rundunar ta mika jaririn da mahaifiyarsa cewa Asibitin Rasheed Shekoni inda likitoci suka tabbatar da mutuwar jaririn.

Shiisu Adam ya ce itama mahaifiyar yarinyar an kwantar da ita a Asibitin domin kula da lafiyar ta.

Advertisement

Ya ce tuni rundunar ta kaddamar da bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending