News
Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta The Association of Online Media Guild Tana Taya Al’ummar Musulmi Murnar Bikin Babbar Sallah
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta The Association of Online Media Guild (ASSOMEG) tana taya daukacin Musulmin Najeriya murnar zagayowar ranar bakin Sallah Babba ta shekarar 2024.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar na riko Abdullateef Abubakar Jos da sakataren riko na Kungiyar Abbas Yushau Yusuf suka fitar a ranar Lahadi, sun ce bikin na bukatar a yi tunani sosai tare da kara rokon Allah Madaukakin Sarki da ya sauwake wa ‘yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta a lokacin daya daga cikin kalubalen da ake fuskanta a wannan lokutan shine matsalar tattalin arziki.
Kungiyar ta kuma yi amfani da wannan damar wajen taya shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano murna sallar.
Sanarwar ta ce kungiyar ta yi kira ga shugabannin biyu da sauran gwamnonin 35 da suka hada da ministan babban birnin tarayya Abuja da su tabbatar sun inganta rayuwar talakawa a wannan mawuyacin lokaci.
Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta The Association of Online Media Guild ta haɗa ɗimbin ma’aikatan watsa labarai ta yanar gizo a duk faɗin Najeriya mai hedikwata a Kano.
