News
Kungiyar ASSOMEG Ta Mika Sakon Ta’aziyya Ga Sanusi Bature Kan Rasuwar Dansa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta The Association of Online Media Guild ASSOMEG ta mika sakon ta’aziyya ga Malam Sanusi Bature, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, bisa rasuwar dansa wanda ya rasu ranar Alhamis yana da shakaru 15.
Wannan babban rashi ne da dukkan mu Mawallafa Jaridun Yanar Gizo mu ke ji, kuma muna cikin baƙin ciki da iyali ke jurewa a cikin wannan mawuyacin lokaci.
Tsadar Man Girki Ya Jefa Mutane Da Dama Cikin Halin Ha’ula’i A Kano
Malam Sanusi Bature ya kasance babban abokin tarayya kuma mai bayar da shawarwari a fagen yada labarai, kuma tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da shi, da iyalansa, da masoyansa.
A madadin daukacin membobin mu, Kungiyar ASSOMEG na mika sakon ta’aziyya ga Malam Bature da iyalansa.
Muna addu’ar Allah ya basu ikon jure wannan rashi da ba za a iya maye gurbinsu da shi ba,
Kuma muna fatan Allah Ta’ala ya sanyawa iyalansa kwanciyar hankali a cikin wannan lokaci na jarrabawa.
