Connect with us

News

Kungiyar ASSOMEG Tana Taya Sabon Shugaban NUJ Murna

Published

on

Kungiyar ASSOMEG Tana Taya Sabon Shugaban NUJ Murna

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo ta The Association of Online Media Guild ASSOMEG ta taya Alhasan Yahaya murna kan zabensa a matsayin sabon Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya wato NUJ.

Advertisement

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da shugaban riko na Kungiyar Abdullateef Abubakar Jos, da sakataren riko, Abbas Yushau Yusuf, suka ka fitar.

Hukumar NAFDAC Ta Gano Wani Jabun Maganin Cutar Maleria Da Ke Yawo A Najeriya

A cikin sanarwar, ASSOMEG ta jinjina wa kwazon Yahaya da jajircewarsa a matsayin mai kawo sauyi, tare da nuna kyakkyawan fata kan jagorantar NUJ cikin nasara. “Muna taya Alhasan Yahaya murna kan zabensa a matsayin sabon Shugaban NUJ. Kwazon sa da jajircewarsa a matsayin mai kawo sauyi abin yabo ne,” sanarwar ta bayyana.

Advertisement

Kungiyar ta kuma jaddada goyon bayan Yahaya wajen ci gaba da inganta aikin jarida a Najeriya da sadaukarwarsa wajen tabbatar da gaskiya da kwarewa.

“Muna da tabbacin cewa ƙarƙashin jagorancinsa, NUJ za ta ci gaba da bunkasa tare da magance kalubalen da suka addabi ‘yan jarida a ƙasar nan,” inji ASSOMEG

Advertisement

Haka kuma, ASSOMEG ta tabbatar da cikakken goyon bayanta ga Yahaya da kuma NUJ, tare da alkawarin yin aiki tare da ƙungiyar domin tallafa wa muradun ‘yan jarida da inganta harkokin watsa labarai a Najeriya.

“Muna fatan yin aiki kafada da kafada da NUJ ƙarƙashin jagorancin Yahaya don cimma burikanmu na bai daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending