Connect with us

News

Babbar Magana: An Sace Wata Mata Mai Juna Biyu A Hanyar Zuwa Asibiti

Published

on

DAGA UASIR SANI ABDULLAHI 

An sace wata mata mai juna biyu mai suna Mrs Ogunbunmi a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Matar wadda aka ce za ta haihu ta bar gidanta da ke Oke Lantoro zuwa babban asibitin jihar, Ijaiye dake Abeokuta,sai dai an yi garkuwa da ita a hanya.

Zargin Ɓatanci : An Hallaka Wani Mutumi A Jihar Bauchi

Mijinta, Ogunbunmi Lateef, ya ce ya samu sakon WhatsApp da ke sanar da shi sace matarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi cikakken bayani ba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, a ranar Alhamis, ta ce, “Wani Ogunbunmi Lateef na Oke Lantoro ya ruwaito cewa matarsa mai juna biyu da za ta haihu ta bar gida zuwa Asibitin Jihar Ijaiye Abeokuta.

Advertisement

Ogun na daya daga cikin jihar da ke fama da yawaitar laifuka a yankin Kudumaso Yamma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending