Connect with us

News

Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Yayi  sanadiyar mutuwar Karamin Yaro Tare Da  Lalata Gidaje 50

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi ya yi sanadiyar mutuwar wani yaro dan shekara 7 a Tsohon Garin Nangere da ke karamar hukumar Nangere a jihar Yobe.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa mutane 20 ne suka samu munanan raunuka, yayin da gidaje da shaguna kusan 50 suka ruguje sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Akalla Mutane Takwas Ne Suka Mutu Yayin Da Wani Gini Ya Rushe A Kano

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin karfe tara na safe lokacin da mazauna yankin ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Advertisement

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe, tare da hadin gwiwar Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL), suka fara wani taron karawa juna sani na matakin Jihohi kan zirga-zirgar jama’a da wayar da kan al’umma kan shirye-shiryen ambaliyar ruwa da samar da shirin tunkarar shirin gaggawa na shekarar 2024.

Makasudin haɗin gwiwar shine, a tsakanin sauran abubuwa, raba hanyoyin mayar da martani na gida, haɗa dabarun tushen al’umma zuwa yunƙurin matakin jiha, da haɓaka shirin shirye-shiryen gaggawa na tushen al’umma.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending