News
Da dumi dumi: Shugaban kasa Bola tinubu ya sake yiwa mutum goma babban mukamai
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin wasu ‘yan Najeriya a hukumar kula da gidaje ta ta Nigeria wato Family Homes Funds Limited (FHFL).
Mai magana da yawun Shugaban kasar , Ajuri Ngelale ya fadi Hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata Daya fitar
Sanarwar tace a a kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na karfafa ayyukan da ke da nufin samar da damar ci gaba a cikin harkokin gidaje”.
Sunayen wadanda aka nada sune
(1) Mista Demola Adebise – Shugaban Hukumar
(2) Malam Abdul Muttalab – Babban Jami’in Gudanarwa
(3) Malam Abdullahi Musa – Babban Darakta (Finance)
(4) Mista Emeka Henry Inegbu – Babban Darakta (Ayyuka)
(5) Wakilin Ma’aikatar Kudi –
(6) Wakilin Hukumar Kula da Zuba Jari ta Najeriya
Sai Kuma ragowar da zasu ringa baiwa hukumar gudun mawa
(7) Mista Sam Okagbue
(8) Malam Musa Ahmed
(9) Dr. Eniang Nkang
(10) Malama Bilkisu Usman
Sanarwar ta ce: “Shugaban yana sa ran sabbin mambobin kwamitin na wannan muhimmiyar hukuma za su yi amfani da kwarewarsu, da gogewa, da kuma jajircewarsu wajen tafiyar da Asusun Gidajen Iyali domin cimma burinsa na bunkasa ci gaba da cigaba a bangaren gidaje”.
