Connect with us

News

Rikicin masarautun Kano : kotu ta haramtawa louyoyi hira da Yan jarida har sai bayan kammala hukunci

Published

on

Rikicin masarautun Kano kotu ta umarci lauyoyin dasu daina hira da manaima labarai

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

babbar kotun jihar Kano da ke zaune a sakatariyar Audu Bako, Kano, ta umurci lauyoyi a rikicin masarautu da su daina yin magana da manema labarai.

Advertisement

Alkalin kotun ta bayar da wannan umarnin ne a lokacin da ake ci gaba da shari’ar, a ranar Alhamis.

Ta ce, “Umarni ne gare ku lauyoyi da kada ku sake yin wata hira da manema labarai kafin da kuma bayan yanke hukuncin kan dambarwar da akeyi wanda ake kara na farko ya daukaka kara”.

Advertisement

 

Mai shari,ar  tace kotu batada da hurumin dakatar da Yan jarida akan ayyukan su Amman kotun tanada hurumin da Zata Hana lauyoyin magana da Yan jarida

Advertisement

Jaridar historical ruwaito cewa jim kadan bayan wannan umarni da , alkalin kotun ta baiwa lauyoyin kotun ta tafi hutu domin yanke hukunci kan takaddamar.

Idan dai za a iya tunawa, Babban Lauyan Jihar Kano, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar Kano, ne suka shigar da karar ta bakin Lauyan su Ibrahim Isah-Wangida, Esq.

Advertisement

 

A karar suna neman kotu ta hana Aminu Ado Bayero da sarakunan Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye cigaba da ayyana kansu a matsayin Sarakuna .

Advertisement

 

Wadanda suka hada da Alhaji Aminu Ado-Bayero da Alhaji Nasiru Ado-Bayero Bichi Sarkin Karaye da Dr Ibrahim Abubakar ll da Sarkin Rano Alhaji Kabiru Muhammad-Inuwa da Alhaji Aliyu Ibrahim-Gaya Sarkin Gaya.

Advertisement

Sauran wadanda ake kara sun hada da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Darakta Hukumar DSS, Jami’an Tsaron Civic defense da rundunar Sojojin Najeriya.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending