Connect with us

News

Kotun Ƙoli za ta yanke hukunci kan ‘yancin ƙananan hukumomi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A yau ne Ƙotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan ƙarar da gwamnatin tarayyar ta shigar gabanta tana buƙatar jihohi su bai wa ƙananan hukumomin ƙasar ‘yancin gashin kai.

Advertisement

Tuni dai kotun da aike wa lauyoyin duka ɓangarorin da ke cikin shari’ar.

Allah Ne Kadai Zai Iya Magance Rikicin Siyasar Da Ke Tsakanin Gwamnan Jihar Ribas Da Nyesom Wike —Shehu Sani

Gwamnatin Najeriyar dai ta maka gwamnonin jahohin 36 a gaban kotu inda ta ke ƙalubalantar su yadda suke take haƙƙin ƙananan hukumomi da ya danganci zaɓe da ba su damar amfani da kuɗaɗen gudanarwarsu.

Advertisement

 

Sai dai gwamnonin sun buƙaci kotun da ta yi watsi da wannan buƙatar da gwamnatin tarayya ta shigar.

Advertisement

 

Gwamnatin tarayyar na kuma son kotun ƙolin ta bayar da umarnin tura wa ƙananan hukumomin kuɗinsa kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya, kamar yadda kundin tsari mulkin ya tanadar.

Advertisement

A Najeriyar ƙananan hukumomin sun jima suna ƙorafin cewa gwamnonin jihohin ƙasar na riƙe musu kuɗaɗensu, lamarin da suka ce shi ke janyo musu rashin gudanar da ayyukan ci gaba a yankunansu.

Masana dai sun jima suna kiraye-kirayen bai wa ƙananan hukumomin ‘yancin gashin kai, kasancewa ƙananan hukumomin sun fi kusanci ga jama’a, masanan na ganin hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan ci gaba a matakin farko.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending