Connect with us

News

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf Ya Naɗa Sababbin Sarakuna A Gaya Da Rano Da Ƙaraye

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa sababbin sarakuna masu daraja ta biyu a jihar.

Advertisement

Waɗanda aka naɗa ɗin su ne Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya, wanda kafin naɗinsa shi ne tsohon Sarkin Masarautar Gaya da aka rushe.

Raba Tirela 20 Na Shinkafa Da Gomnatin Tarayya Ta Yiwa Jahohi Ba Shine Ma Fita Ga Talakawan Nigeria Ba

Sai Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin naɗinsa shi ne hakimin Rogo.

Advertisement

Sai kuma Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Sarkin Rano, wanda kafin naɗinsa shi ne hakimin Bunkure.

Wata sanarwa da kakakin gwamnan na Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce naɗin ya fara aiki nan take.

Advertisement

“Yayin da yake musu murna bisa naɗin, Gwmana Abba K. Yusuf ya yi kira a gare su su kasance masu kiyaye al’adu da zaman lafiya da haɗin kan jama’arsu.

A ranar Talata ne Gwamna Abba ya sanya hannu kan sabuwar dokar Masarautun Kano wacce ta ƙirƙiri Masarautun Gaya da Rano da Ƙaraye masu daraja ta biyu.

Advertisement

Gwamnan ya saya hannu kan sabuwa dokar ne ‘yan sa’o’i bayan Majalisar Dokokin Jihar ta amince da sabuwar Dokar Masarautun a ranar Talata.

Sababbin masarautun za su ƙunshi wasu ƙananan hukumomi ne a ƙarƙashinsu, sai dai ya yawan ƙasashen hakiman bai kai na tsofaffin masarautun da aka rushe ba.

Advertisement

Sanarwar da Sanusi Bature ya fitar ta ce a yanzu “Masarautar Gaya za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu ne kawai. Rano za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure kawai, yayin da Ƙaraye za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Ƙaraye da Rogo kawai.”

Naɗa sabbin sarakunan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tirka-tirka kan dokar da gwamnatin jihar ta sanya wa hannu ta rushe masarautu hudu na Gaya da Rano da Karaye da kuma Bichi, da sauke Sarki Aminu Ado Bayero da kuma mayar da Sarki Muhammadu Sanusi na II.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending