News
Raba Tirela 20 Na Shinkafa Da Gomnatin Tarayya Ta Yiwa Jahohi Ba Shine Ma Fita Ga Talakawan Nigeria Ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Raba Tirela 20 Na Shinkafa Da Gomnatin Tarayya Ta Yiwa Jahohi Ba Shine Ma Fita Ga Talakawan Nigeria Ba
Ku a lokacin baya sai da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kai samame a wani dakin ajiyar kaya da gwamnatin jihar ta raba sama da buhu 1,000 na masara yayin da aka karkatar da kayan abinci tare da ajiyewa.
Jaridar Inda Ranka ta samu labarin cewa gwamnan ya fasa rumbun ajiyar kaya, dake unguwar Sharada Industrial a cikin birnin Kano a ranar 2 ga watan December 2023
Rahotanni na nuni da cewa a lokacin COVID-19 an yi makamancin haka gomnatin tarayya ta bada tallafi wa gomnoni domin su rabawa talakawa amma da yawa gomnoni ba su raba ba, sai lokacin ya kin neman zaɓe suka fito suka raba domin a zaɓe su.
Da wannan kame-kame da Gwamati take yi gwara a dawo da tallafin man fetur domin shine abinda gomnati zata yi ya amfani talakan Nigeria, ƙasa tana fama da yunwa da matsalar tsaro kuma ace talaka ba zaiyi magana.
Sai dai Fitaccen malamin addinin Muslunci Sheik Ibrahim Khalil ya ce “Wannan abu da matasa suka motso dashi yanzu za’a godewa Allah cewar sun gane rayuwa yanzu, kuma muna fatan zasu daina karbar Taliya ko shinkafa suyi zabe”.
Sheik Ibrahim Khalil ya bayyana hakan a cikin wani sakon bidiyo daya wallafa a shafinsa na Facebook mai take Zanga-Zanga.
Inda ya bayyana cewar “wannan abu da matasa suka motso dashi a yanzu abin murna ne domin ya nuna cewar sun fara banbance dadi da wahala”.
“Wannan abu da matasa suka motso dashi yanzu za’a godewa Allah cewar sun gane rayuwa yanzu, kuma muna fatan zasu daina karbar Taliya ko shinkafa suyi zabe”.
Inda kuma yayi kira ga matasan dasu guji zagin malamai da shugabanni domin hakan tamkar guba ce ga rayuwarsu.
