News
Muna Goyon Bayan Haramta Ayyukan Haƙar Ma’adinai – Rundunar Sojojin Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa za ta goyi bayan hana haƙar ma’adinai na wani lokaci, domin a samu damar magance matsalar tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a cikin ƙasar nan.
Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Christopher Musa ne bayyana haka ranar Litinin, a lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Kula da Ma’adinai.
Kwamitin ya na bincike ne kan ayyukan masu haƙar ma’adinai ba da lasisi ba.
Musa bai samu damar halarta ba, amma ya tura wakilcin Daraktan Gudanarwa na Hedikwatar Tsaro, Nnaemeika Ignatius. Ya ce Sojojin Najeriya na goyon bayan dakatar da haƙar ma’adinai tsawon shekaru ɗaya a Najeriya.
Wannan matsayar da sojojin suka bayar ta biyo wata magana da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, Julius Ihonvbere, wanda ya ce Majalisar Tarayya za ta ɗauki tsauraran matakai a kan harkokin haƙar ma’adinai.
Musa ya ce tabbas akwai alaƙa tsakanin matsalar tsaro da kuma masu haƙar ma’adinai ta haramtacciyar hanya.
Ya ce akwai raɗe-raɗin cewa ana amfani da ta’addanci ne da ‘yan bindiga kawai domin a yi wa haramtacciyar sana’ar haƙar ma’adinai rumfar kariya.
Ya ce sojoji na ci gaba da kama ‘yan ƙasashen waje masu haƙar ma’adinai ba tare da lasisi ba a cikin ƙasar nan.
Shugaban Kwamitin Kula da Harkokin Ma’adinai, Jonathan Gaza, ɗan SDP daga Jihar Nasarawa, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta ce ta yi asarar dala biliyan 9 sanadiyyar haƙar ma’adinai ba tare da lasisi ba.
