News
Cutar Kwalara Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane AKALLA 103, YAYIN DA SAMA DA 3,000 SUKA Kamu Da Cutar A Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Adadin wadanda suka mutu sanadiyar cutar amai da gudawa ya kai 103 a Najeriya, yayin da sama da mutane 3,000 suka kamu da cutar
Barkewar cutar kwalara a Najeriya ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 103, yayin da sama da 3,000 da ake zargin sun kamu da cutar.
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Kafa Masarautu Masu Daraja Ta Biyu
Channels tv ta ruwaito cewa Darakta Janar na Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Jide Idris, ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
Ya kara da cewa yanzu haka an samu bullar cutar a fadin kananan hukumomi 187 dake cikin jihohi 34 da kuma babban birnin tarayya Abuja.
A cewar shugaban NCDC, jihohi shida da ke kan gaba wajen bayar da kashi 83 na masu kamuwa da cutar sun hada da Legas, Bayelsa, Abia, Ebonyi, Katsina da Zamfara.
Ya alakanta kamuwa da cutar da ambaliyar ruwa da ake samu a wasu jihohin kasar nan, da cin gurbataccen abinci da ruwa da kuma bayan gida a fili.
Haka zalika Ya shawarci ‘yan Najeriya da su rika tsaftar muhalli tare da yin taka-tsan-tsan wajen kamuwa da cututtuka masu yaduwa a lokacin damina.
