News
Hukumar JAMB ta bayyana sunayen jami’o’in da ke ɗaukar ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a (JAMB) ta zargi wasu jami’o’i da laifin karya dokoki da ƙa’idojin ɗaukar ɗalibai.
Rajistara na JAMB, Is-haq Oloyede ne ya yi wannan zargin a ranar Alhamis, yayin wani taron tsare-tsaren ɗaukar ɗalibai cikin jami’o’i, a Abuja.
Najeriya Ta Ci Tarar Facebook Da Whatsapp $220m Kan Karya Dokar Kare Sirrin Mutane
Jami’o’in da ya zarga sun haɗa da Jami’ar Nsukka (UNN), Jami’ar Abuja (UNIABUJA), NOUN, Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) da kuma Jami’ar Jihar Delta (DELSU).
Taron dai ya ƙunshi shugabannin jami’o’in ƙasar nan da rajistarori, shugabannin Manyan Kwalejojin Fasaha da kuma na Manyan Makarantun Ilimi Mai Zurfi.
Oloyede ya ce tuni dai Ma’aikatar Harkokin Ilmi ta Ƙasa ta yafe wa ɗalibai har miliyan 1 da aka ɗauka a waɗannan jami’o’i ba bisa ƙa’ida ba, tsakanin 2017 zuwa 2020.
“To amma kuma duk da haka, waɗannan jami’o’i ba su daddara ba, sun ci gaba da ɗaukar ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba,” cewar Oloyede.
Ya ce daga cikin ɗalibai miliyan ɗaya da aka ɗaga wa ƙafa, JAMB ta ɗauki 600 kaɗai, amma sauran duk ba su cika sharuɗɗa da cancanta ba.
Ya ce akwai wasu 700 kuma da aka ɗauka a waje ba a cikin tsarin JAMB ba.
Ya zargi jami’o’in da bai wa ɗalibai takardar shaidar ɗauka tun kafin a kammala tantance cancantar su a shekarun 2020, 2021, 2022 da 2023.
Ya ce duk jami’ar da ta ɗauki ɗalibai da gangan bayan ɗaga ƙafar da aka yi cikin 2020, to ita ta ja wa kan ta.
Premium Times
